Isa ga babban shafi
Syria

An tsagaita wuta na kwanaki 4 a Syria

Dakarun Sojin Syria sun sanar da tsaigata bude wuta a yankunan da ake yaki a kudancin kasar wanda ke zuwa adai-dai lokacin da ake shirin sake komawa teburin tattaunawar sulhu a birnin Astana da ke Kazakhstan.

An tsagaita wuta a wasu yankunan Syria
An tsagaita wuta a wasu yankunan Syria AFP
Talla

Wata sanarwa da aka fitar a kafar yadda labaran kasar Syria ta SANA, ta ce za a dakatar da yaki a yankunan Daraa, Quneitra da Sweida, na tsawon kwananki 4 don nuna goyon baya samar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

Sai dai hakan bai shafi yakin da sojin ke yi da kungiyar IS ba.

Kungiyar da ke saido kan yankin Syria da ke Britaniya, ta tabbatarwa kamfanin dilancin labaran Faransa, AFP, cewa a yanzu babu wani tashin hankali ko hari da aka kai tun bayar sanar da tsaigata wuta a yankunan guda 3.

Sai dai a cewar Kungiyar, Dakarun basu Ambato taron Astana da, da za a shafe tsawon kwananki 2 ana gudanarwa.

A lokacin taron manema labarai kafin wannan rana, mataimakin Ministan harkokin wajen Syria, Faisal al-Moqdad, ya ce wajibi ne su halarci taron don gani an kawo karshan zub da jinni a Syria.

Kazalika wakilin ‘yan tawayen kasar, Janar Ahmad Berri, ya tabbatarwa kamfanin dilancin labaran Faransa, AFP, cewa zai halarci taron.

Bayan Taron Astana, akwai zaman tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya da za a soma cikin tsakiyar Yuli a Geneva kan kasarta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.