Isa ga babban shafi
MDD

Amurka ta kashe fararen hula 300 a Raqqa inji MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare haren jiragen sama da Amurka ke jagoranta sun kashe fararen hula 300 a garin Raqqa da ke arewacin Syria.

Mutane da yaki ya raba da matsuguni a Raqqa da ke Syria
Mutane da yaki ya raba da matsuguni a Raqqa da ke Syria REUTERS/Rodi Said
Talla

Ofishin da ke binciken laifukan yaki na MDD ya bayyana damuwa kan yawan adadin fararen hular da aka kashe a yayin da jiragen yaki ke wa IS luguden wuta a Raqqa.

Hukumar binciken laifukan yakin ta ce daruwan fararen hula aka kashe a lardin Raqqa a hare haren sama da Amurka ke taimakawa ‘Yan tawaye Syria da kurdawa domin kwato yankin daga mayakan IS.

Ofishin na MDD ya ce fararen hular sun shiga tsaka mai wuya ne, tsakanin hatsarin IS da kuma hare haren sama da ke rutsawa da su.

Hukumar ta ce ta tattara adadin fararen hular 300 da aka kashe tun kaddamar da hare haren na sama, a ranar 1 ga watan Maris.

Wata jami’ar hukumar tace a cikin rana daya an kashe fararen hula 200 a harin da aka kai garin Al Masura ranar 21 ga Maris.

Hukumar ta ce adadin fararen hular da suka mutu na iya zarce haka, saboda sun tattara alkalumman mamatan ne ba tare da samaun izinin shiga Syria ba.

A 2014 ne dai IS ta karbe ikon garin Raqqa wanda ta bayyana a mastayin daula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.