Isa ga babban shafi
Japan

Majalisar Japan ta amince Sarki Akihito ya yi murabus

Majalisar Japan ta amince da dokar da za ta ba Sarki Akihito yin murabus, wanda shi ne karon farko a shekaru sama da 200 da Sarkin Japan zai sauka kafin mutuwarsa.

Sarki Akihito na Japan
Sarki Akihito na Japan REUTERS/Issei Kato
Talla

A kwanakin baya ne Sarki Akihito mai shekaru 83, wanda ya shafe kusan shekaru 30 kan gadon sarauta, ya bayyana bukatar yin murabus saboda tsufa da matsalolin rashin lafiyarsa.

Matakin dai ya haifar da kalubale a Japan saboda babu wata doka da aka yi tanadi idan Sarki zai yi murabus kafin kwanansa ya kare a gadon sarautar kasar.

Kudirin ya samu amincewar babbar majalisar Japan da gagarumin rinjaye a yau juma’a bayan karamar majalisar ta amince a makon jiya.

Amma sai nan da shekaru uku Sarki Akihito zai yi murabus, dokar da a karon farko ta hau kansa shi kadai.

Jaridun Japan sun ce a 2018 Sarkin zai yi ritaya daga gadon sarauta.

Batun murabus din sa ya janyo muharawa saboda muhimmacin sarautar a Japan.

Wasu na ganin siyasa na iya tasiri a masarautar idan har aka kafa dokar da za ta ba sarki damar yin murabus.

Ana tunanin Dan sa na farko Naruhito mai shekaru 57 za a nada sarki. Amma wasu ganin nan gaba saurautar na iya koma ga Mata idan har jikan Sarki Akihito bai haifi namiji ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.