Isa ga babban shafi
Iran

IS ta kashe mutane 12 a hare-haren hubbaren Khomeini da Majalisar Iran

Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon tagwayen hare-hare da aka kai wa Majalisar dokokin Iran da kuma hubbaren jagoran juyin-juya halin kasar a wannan Laraba.

Jami'an tsaron Iran na gudu a lokacin da aka kai hari Tehran
Jami'an tsaron Iran na gudu a lokacin da aka kai hari Tehran REUTERS
Talla

Tuni Kungiyar IS da ke da’awar jihadi ta dauki alhakin kai hare haren bayan ta watsa bidiyon maharan a kafar Amaq da ta ke amfani wajen yada Farfaganda.

Adadin mutane 39 suka jikkata a jerin hare haren guda biyu da aka kai a Tehran a yau Talata.

‘Yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, a Majalisar Iran yayin da kuma wasu maharani daban suka tayar da bama-bamai a hubbaren jagoran juyin juya halin kasar Ayatollah Khomeini.

IS ta nuna bidiyon mutanen da ta ce mayakanta ne a lokacin da suke kai farmakin a Majalisr Dokokin Iran.

Jami’an ‘yan sandan Iran sun bayyana cewa, an kashe ilahirin maharan bayan shafe sa’oi biyar ana dauki ba dadi da su.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce, mayakan sun yi shigar burtu, in da suka sanya kayan mata kafin shiga harabar Majalisar Dokokin.

A lokaci guda ne dai maharan suka kai tagwayen hare-haren a Majalisar da kuma hubberen Khomei da ya jagoranci juyin juya halin kasar a shekarar 1979.

Kasar Iran dai na goyon bayan Iraq da kuma shugaban Syria Bashar al-Assad wajen yaki da kungiyar ISIS.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana hare-haren da IS ke kai wa a Nahiyar Turai a matsayin tasirin tsare-tsaren kasashen Yamma a yankin gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.