Isa ga babban shafi
Qatar

Manyan kasashen Larabawa 4 sun yanke hulda da Qatar

Kasashen Saudi Arabiya da Bahrain da Masar da Daular Larabawa sun sanar da katse huldar diflomasiya da kasar Qatar sakamakon barakar da ta barke tsakanin kasashen da ke Yankin tekun Fasha.

Doha babban birnin Qatar
Doha babban birnin Qatar REUTERS/Fadi Al-Assaad/File Photo
Talla

Kasashen sun zargi Qatar da taimakawa ayyukan ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran Saudiya ya ruwaito cewar bayan katse huldar diflomasiyar, kasar ta kuma rufe iyakokinta da Qatar kana bin da ta kira kare kare kanta daga hare haren ta’addanci.

Masar ta ce sakamakon daukar wannan matakin, za ta rufe tasoshin jiragen sama da na ruwa ga jiragen Qatar.

Bahrain da kasar Daular Larabawa ma sun katse hulda da Qatar.

Bahrain da zargi Qatar da haifar da matsalar tsaro a cikin kasarta tare da shiga sha’anin harakokin cikin gidanta.

Kasashen kuma sun kori Qatar daga cikin kawancen kasashen larabawa da Saudiya ke jagoranta wajen yakar ‘yan tawayen Yemen.

Kasashen sun zargi Qatar da taimakawa kungiyoyin ta’adda da suka hada da al Qaeda da kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a Syria da Iraqi.

A makwannin da suka gabata ne kafofin yada labaran Amurka suka wallafa wani rahoto da ke zargin Qatar da daukar nauyin ta’addanci.

Qatar ta musanta zargin tare da kaddamar da bincike akan kutsen da ta ce an yi wa kamfanin dillacin labaranta inda aka buga labari game da alakarta da Iran da kuma hasashen cewa Trump ba zai jima ba a matsayin shugaban Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.