Isa ga babban shafi
Bangladesh

Guguwar Mora ta afka wa jama'ar Bangladesh

Hukumomin Bangladesh sun ce, akalla mutane kusan miliyan guda aka kwashe daga gidajensu kafin wata mummunar guguwa ta doshi yankunan da suke rayuwa. 

Mummunar guguwa ta afka wa Bangladesh
Mummunar guguwa ta afka wa Bangladesh AAP/Sarah Motherwell/via REUTERS
Talla

Ana saran guguwar da aka yi wa lakabi da Mora ta afka wa birnin Chittagong mai tashar jiragen ruwa da ke yankin gabashin kasar.

Abul Hashim mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta kasar ya tabbatar da kwashe mutanen, in da aka kai su tundun mun-tsira.

Jami’in ya ce, guguwar mai tafe da ruwan sama da tsawa na tafiyar kilomita 135 a cikin sa’a guda, yayin da ta rusa dubban gidaje.

Kawo yanzu dai babu rahotannin da ke nuna asarar rayuka sakamakon guguwar, amma hukumomin kasar sun tabbatar cewa, ta yi barna sosai a birane da kauyuka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.