Park ta musanta aikata laifi a Koriya ta Kudu
Tsohuwar shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye ta musanta aikata ba dai dai ba a tuhumar da aka fara yi ma ta kan zargin aikata wasu laifuka da suka hada da cin hanci da rashawa.
Wallafawa ranar:
Uwargida Park da aka tsige da aka tsige daga karamar mulki na fuskantar tuhume-tuhume kan cin hanci da rashawa da tozarta karfin mulki da kuma fallasa sirrikan kasa.
A karon farko kenan da tsohuwar shugabar ke bayyana a bainal jama’a tun bayan cafke ta a cikin watan Maris da ya gabata.
Jami’an ‘yan sandan kasar sun sanya ma ta sarka a hannunta a yayin taso keyarta zuwa kotun birnin Seoul cikin motar daukan fursunoni.
Ana zargin Park Geun-hye da hada kai da aminiyarta, Choi Soon-sil wajen karbar kudade daga wasu manyan Kamfanonin kasar da suka hada da Samsung da nufin yi mu su alfarmar siyasa.
Koriya ta Kudu na da damar yanke hukuncin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu