Isa ga babban shafi
China

Taron farfado da hanyoyin kasuwanci a Duniya a China

Kasar China na ci gaba da sabon yabo saboda yunkurin da tayi na bunkasa harkokin kasuwancin ta a duniya.Akalla shugabanin kasashe 30 ke halartar taron kwanaki biyu da ake gudanar a Beijing kan farfado da hanyoyin kasuwanci da akayi tsakanin Asia da Turai da Afirka, kuma cikin mahalarta taron harda shugaban Rasha Vladimir Putin da na Turkiya Recep Tayyip Erdogan. 

Taron farfado da hanyoyin kasuwanci a Duniya a China
Taron farfado da hanyoyin kasuwanci a Duniya a China REUTERS/Wang Zhao/Pool
Talla

Shugaba Xi Jinping a wajen bude taron ya yi tayin zuba Dala biliyan 124 wajen inganta tashoshin jiragen ruwa da na kasa da hanyoyin motoci.
Sakataren kudin Birtaniya Philip Hammond ya ce a shirye suke suyi aiki tare.
Ana sa ran Shugabanin kasashe dake halartar wannan taro na China za su samar da hanyoyin ceto tattalin arziki da ma bunkasa kasuwanci a kasashen ma su tasowa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.