Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Shugaba Trump ya samu ganawa da Lavrov

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Rasha ta zama alkibla ga shugaban Syria Bashar al Assad da kuma aminiyar shi Iran, a ya yin da Washington da Moscow ke kokarin fahimtar juna kan rikicin na Syria.Trump ya fadi haka ne bayan ganawarsa da Sakataren harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov. 

Ministan harakokin wajen Rasha Serguei Lavrov da Shugaban Amurka Donald Trump
Ministan harakokin wajen Rasha Serguei Lavrov da Shugaban Amurka Donald Trump
Talla

Shugaba Trump ya ce sun yi ganawa mai ma’ana da Lavrov a fadarsa , tare da cewa sun amince su yi kawo karshen zubar da jinnin da ake yi a Syria.

Sakataren harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya kasance babban jami’in gwamnatin kasar da ya kai ziyara Washington tun lokacin da aka rantsar da Trump a watan Janairu.
Trump ya sheidawa Lavrov cewa ya na son Rasha ta kasance jagora da alkiblar shugaban Syria Bashar al Assad da kuma Iran aminiyarsa.

Lavrov dai ya tafi Washington ne domin neman goyon bayan Amurka kan bukatar Rasha na amincewa kan haramta shawagin jirage a Syria da zai taimaka wajen bude kofar tattaunar kawo karshen ricikin tsakanin gwamnatin Assad da kuma ‘yan tawaye.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.