Isa ga babban shafi
India

Aure: Kotun kolin India ta fara nazari kan furucin saki uku

Kotun Kolin India ta fara nazari kan korafe korafen da aka shigar a gabanta da ke kalubalantar sharuddan sakin aure a tsarin addinin Islama da aka ba maza damar rabuwa da matansu nan take bayan sun furuta "na sake ki saki uku".

Wasu Matan Musulmi sun soki furucin saki uku nan take a India
Wasu Matan Musulmi sun soki furucin saki uku nan take a India REUTERS/Cathal McNaughton
Talla

Kundin tsarin mulkin India ya ba musulmi ‘yancin sakin matansu saki uku bisa tsarin addininsu na Islama.

Amma batun furucin saki uku da maza ke yi nan take ya janyo muhawara da cece-kuce a kasar inda rahotanni suka ce maza sun koma suna sakin mata a kafofin sadarwa na intanet ta hanyar rubuta wasika a whatsapps da Skype.

Matan aure da dama da aka saka ne ke kalubalantar tsarin inda suka bukaci kotun koli ta diba ta kuma soke hukuncin saboda ya sabawa addinin Islama.

Akwai dai Malaman addinin Islama da ke fatawa akan furucin saki uku nan take na a matsayin saki guda ne. Sai dai a yi sakin daki daki, daga daya zuwa biyu zuwa uku.

Yanzu Kotun Kolin ta fara nazari kan ko furucin saki uku nan take  ya inganta a addinin Islama.

Sai dai kungiyoyin musulmi da dama a India na sukar kotun kan shiga sha’anin addininsu.

A ranar 19 ga watan Mayu ne Kotun za ta kammala sauraren karar kafin zartar da hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.