Isa ga babban shafi
China

China ta yi nasarar gwajin jirgin fasinjanta

China ta samu nasarar gwajin jirgin fasinjanta na farko a yau Juma’a wanda aka kera a kasar, da nufin shiga gogayya da manyan kamfanonin jiragen sama na duniya.

Jirgin fasinja kirar China
Jirgin fasinja kirar China REUTERS
Talla

An shafe shekaru China na kera jirgin da ake kira COMAC, wanda zai taimakawa kasar rage dogaro da jiragen Airbus na Turai da kuma Boeing na Amurka.

Jirgin mai suna C919, mai fenti fari da ratsin fenti bula da kore ya cira ne daga tashar Pudong ta birnin Shanghai.

Dubban mutanen China ne suka yi dafifi domin ganin yadda jirgin kirar kasar ya tashi.

Jirgin ya shafe sama da sa’a daya yana shawagi a sama kafin ya sauka.

An karrama direbobin da suka yi gwajin a yau da faranni, yayin da mutane suka yi ta murna da nuna farin cikin nasarar gwajin jirgin..

China ta dage kan samar da jirginta domin shiga hammaya da na Turai da Amurka da ta jima tana dogaro da su.

Tun a 1970 China ta fara tunanin kera jirgin sama mallakinta.

Kuma yanzu kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta duniya tayi hasashen cewa kasuwar jirgin na China zai sha gaban Boeing na Amurka da kuma Airbus na Turai.

Amma kuma China na bukatar jirage kusan dubu 7 domin gogayya a kasuwar ta zirga-zirga jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.