Isa ga babban shafi
Japan

Japan za ta sauya kundin tsarin mulkinta

Firaministan Japan Shinzo Abe ya sanar da matakin sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar da Amurkawa suka rubuta bayan kammla yakin duniya na biyu. Matakin na zuwa a yayin da Japan ke cika shekaru 70 da amfani da kundin da ‘yan mamayar Amurka suka rubuta.

Firaministan Japan Shinzo Abe
Firaministan Japan Shinzo Abe Yuya Shino
Talla

Mista Abe ya ce yana fatar soma amfani da sabon kundin tsarin mulkin daga shekarar 2020, lokacin Tokyo babban birnin kasar zai karbi bakuncin wasannin Olympics.

Sai dai Firaministan bai yi cikakken bayani game da sauye sauyen da sabon kundin tsarin zai kunsa ba.

Amma ana sa ran tsaron Japan da kare kai da ‘yancin kaddamar da yaki na daga cikin manyan sauyin da gwamnatin Abe za ta aiwatar a sabon kundin tsarin mulkin.

A tarihi dai ba a taba yi wa kundin tsarin mulkin da Amurkawa suka rubutawa Japan kwaskwarima ba, kodayake gwamnatoci da dama a kasar sun ta fassara kundin yadda zai dace musamman kan batun tsaro.

Yanzu dai majalisa za ta yi muhawara kan kudirin, kafin a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin tabbatar da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.