Isa ga babban shafi
Syria

Assad ya musanta zargin amfani da makamai masu guba

Shugaban Syria Bashar Assad ya musanta zargin yin amfani da makamai masu guba wajen kai wa ‘yan tawayen kasar hari, kamar yadda ya shaidawa Bashar Assad kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP a wata tattaunawa ta musamman.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad Syrian Presidency Press Office / AFP
Talla

“Babu wani dalili da zai sa mu yi amfani da makamai masu guba, domin ba mu da irin makaman da ake zance”, a cewar shugaban na Syria.

Sannan ya ce tun shekaru uku da suka gabata ya salwantar da makaman.

Shugaban ya ce ko da ace Syria na da irin wadannan makamai babu wani dalili da zai sa ya yi amfani da su.

Assad ya zargi Amurka da hada baki da ‘yan tawaye domin da cewa ya kai hari mai guba domin smaun hanyar kaddamar da hare hare.

Shugaban ya ce bayanan da suka gani a kwatunan Talabijin Farfaganda ce kawai yana mai cewa babu wani bincike da aka gudanar amma sai Amurka ta kai harin ramuwa.

A ranar 4 ga Afrilu aka kai harin makaman masu guba inda mutane 87 suka mutu a garin Khan Sheikhun yankin da ‘Yan tawayen Syria ke iko

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.