Isa ga babban shafi
Syria

Kasashe 3 sun mika sabon daftari ga kwamitin tsaro na MDD kan Syria

Birtaniya, Faransa da Amurka sun gabatar da sabon kudurin bukatar a gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake wa gwamnatin Syria na kai hari da makami mai guba kan fararen hula.

Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley rike da hotunan wadanda harin makami mai guba a rutsa da su a garin Khan Shiekhun na Syria, yayin taron kwamitin tsaro na majalisar.
Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley rike da hotunan wadanda harin makami mai guba a rutsa da su a garin Khan Shiekhun na Syria, yayin taron kwamitin tsaro na majalisar. Shannon Stapleton/REUTERS
Talla

Ko a makon da ya gabata, saida kwamitin tsaron majalisar dinkin duniyar ya tattauna kan wasu kudurori 3 kan batun harin Syrian to sai dai ya gaza cimma wata matsaya, sakamakon hawa kujerar naki da Rasha ta yi.

Karkashin sabon daftarin, dole ne gwamnatin Syria ta bayyana muhimman tsare tsaren da ta ke bi wajen aiwatar da ayyukan sojinta a yakin da suke fafatawa da ‘yan tawayen kasar da ma mayakan IS.

Zalika tilas gwamnatin Assad ta bada cikakken hadin kai ga tawagar masu da za’a wakilta don bincikar zargin da ake mata na hallaka fararen hula 87 ciki kananan yara 31 ta hanyar amfani da makami mai guba a garin Khan Shiekhun.

Ko da yake kasar Rasha ta hau kujarar naki kan kudurin da Amurka da Faransa suka gabatar kan Syrian a baya, jakadan Faransa a majalisar dinkin duniya François Delattre, ya ce akwai fatan a wannan karon sabon daftarin ya samu amincewar baki dayan kasashen da ke da kujerar dindindin a kwamitin tsaron majalisar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.