Isa ga babban shafi
India

Dalibai 'yan Afrika na cikin fargaba a India

A ci gaba da hare haren da ake kai wa kan dalibai da ke karatu a India, da suka fito daga nahiyar Afirka, ‘yan sandan kasar sun ce an sake kai hari kan wata daliba ‘yar kasar Kenya.

Dalibai 'yar kasar Kenya mai shekaru 25 da wasu suka ci zarafinta yayinda da take komawa gida a India.
Dalibai 'yar kasar Kenya mai shekaru 25 da wasu suka ci zarafinta yayinda da take komawa gida a India. dailymail.co.uk
Talla

Dalibar ta gamu da ta’addancin ne yayinda take komawa gida a Greater Noida, dake wajen birnin New Delhi.

Babban jami’in ‘yan Sandan yankin Sujata Singh ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A zantawarsa da sashin hausa na RFI, AbdulMajid Mustafa dalibi dan Najeriya dake jami’ar garin ya ce dalibar ta dauki shatar motar haya zuwa gida ne, inda gungun ‘yan ta’addan suka tsayar da mai motar, suka kuma fito da ita tare da yi mata dukan kawo wuka.
A cewar Mustafa, sakamakon haka kungiyar daliban Afrika da ke kasar ta India ta basu umarnin zama a masaukansu, su kuma kauracewa fita ko da zuwa makaranta har sai abinda hali yayi.

Dalibin ya ce tuni kungiyarsu ta sanar da gwamnatin Najeriya halin da ake ciki, kuma har jami’an ofishin jakadancin kasar sun kaiwa dalibar ziyara a asibitin da ta ke karbar magani, sun kuma kaiwa daliban ziyara.

01:28

INDIA-ABDULMAJID MUSTAPHA-1.30sec-2017-03-30

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.