Isa ga babban shafi
Yemen

Mata sun fi shan wahala a rikicin Yemen-MDD

Wani rahoton Asusun tallafawa jama’a na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yakin da ake fafatawa a kasar Yemen ya yi sanadiyar lalata rayuwar mata manya da kanana sama da dubu goma.

Dakarun Gwamnatin Yemen da Saudiya ke taimakawa na yaki ne da 'Yan tawayen Huthi 'yan Shi'a
Dakarun Gwamnatin Yemen da Saudiya ke taimakawa na yaki ne da 'Yan tawayen Huthi 'yan Shi'a ©REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Rahoton ya ce rayuwar mata a kasar Yemen ya zama abin tausayawa saboda rashin samun kariya daga cin mutuncinsu.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da ake cika shekaru biyu da fara yakin kasar Yemen, inda rahoton na hukumar UNFPA ya ce tozarta mata ya karu da kashi 63% a shekaru biyu da suka gabata.

A cewar rahoton ayyukan ashsha da ake yi wa mata sun karu sosai, da suka hada da fyade da fada a gida da auren tilas.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a yanzu haka mabukata agaji a kasar ta Yemen sun karu sosai zuwa kusan miliyan 19, yayin da sama da mutane miliyan 10 ke matukar bukatar tallafi.

Saudiya ce ke jagorantar hare hare ta sama akan ‘yan tawayen Huthi a Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.