Isa ga babban shafi
Iraqi

Sama da mutane 45,000 sun tsere daga yammacin Mosul

Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta Duniya IOM ta ce zuwa yanzu sama da mutane 45,000 ne suka tsere daga yammacin Mosul, tun bayan kaddamar da sabon farmakin kwato yammacin birnin a ranar 19 ga watan Fabarairu da sojin Iraqi suka yi.

Wasu fararen hula da ke tserewa fadan da ake gwabzawa a yammacin birnin Mosul.
Wasu fararen hula da ke tserewa fadan da ake gwabzawa a yammacin birnin Mosul. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Kididdigar hukumar ta IOM ta nuna cewa, sama da fararen hula 17,000 ne suka isa sansanin ‘yan gudun hijirar da aka tanada a wajen birnina ranar 28 ga watan fabarairu.

A ranar 3 Juma’ar da ta gabata kuwa, sama da mutane 13,000 ne suka tsere daga yammacin birnin na Mosul.

A jimlace dai hukumar lura da ‘yan gudun hijirar ta IOM, ta ce zuwa yanzu sama da mutane 200,000 ne sabon farmakin kwato yammacin Mosul daga hannun mayakan IS ya raba da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.