Isa ga babban shafi
Faransa

Francois Fillon na tunanin sauka daga takarar shugaban kasa

Dan takarar shugabancin Faransa karkashin inuwar Jam’iyyar Republican Francois Fillon ya yi alkawarin janyewa daga takara muddin aka kaddamar da binciken sa a hukumance.

Francois Fillon na jam'iyyar Republican.
Francois Fillon na jam'iyyar Republican. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Hakan ya biyo bayan zargin da ake yi wa Mista Fillon da biyan matarsa da ‘ya’yan sa albashi kan wani aiki, zarge-zargen da ya sha musantawa.

Ana shirin soma gudanar da bincike sai dai har yanzu ba’a kai ga tabbatar da shi ba a hukumance, wannan na zuwa ne a yayin da ya rage makwanni takwas a gudanar da zaben kasar.

Fillon shine tsayayye a jam’iyyar Republican mai adawa, da ake sa ran zai iya lashe zaben sai dai zarge-zargen cin hanci da rashawa ya mamaye dan takarar wanda kuma babban koma baya ne ga burinsa na mulkin kasar ta Faransa,.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.