Isa ga babban shafi
Pakistan

IS ta kashe mutane 70 a Pakistan

Kungiyar Mayakan ISIS ta dauki alhakin kai kazamin harin da ya hallaka mutane sama da 70 yayin da sama da 200 suka jikkata a wani wurin ibada da ke Pakistan.

Wurin Ibadar Shahbaz Qalandar, a Sehwan inda IS ta kai hari a Pakistan
Wurin Ibadar Shahbaz Qalandar, a Sehwan inda IS ta kai hari a Pakistan REUTERS/Akhtar Soomro
Talla

Wannan shi ne hari mafi muni da aka samu a cikin wannan shekara.

Bayanai sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya kutsa kai wurin ibadar Shahbaz Qalandar, wani Sufi da akayi a karni na 13, inda ya tada bam a cikin taron daruruwan jama’a.

Wurin ibadar na garin Sehwan a Yankin Sindh da ke da nisan kilomita 200 daga birnin Karachi.

Harin ya sa gwamnatin Pakistan rufe iyakarta da Afghanistan, musamman ganin kasashen biyu sun dade suna zargin juna da baiwa yan ta’adda mafaka.

Ministan lafiya Sikandar Ali Mandhro ya tabbatar da mutuwar mutane sama da 70, yayin da 250 suka samu raunuka daban daban.

Wani shaidar gani da ido yace bam din ya daidaita sassan jikin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.