Isa ga babban shafi
Yemen

Dakarun Yemen sun kwato garin Mokha

Rundunar sojin gwamnatin Yemen ta yi nasarar karbe ikon garin Mokha da ke gabar tekun Maliya daga hannun ‘yan tawaye bayan kwashe tsawon lokaci ana fafatawa a tsakanin bangarorin biyu.

Dakarun Yemen sun kwato garin Mokha.
Dakarun Yemen sun kwato garin Mokha. REUTERS/Stringer
Talla

A yau juma’a aka kawo karshen arangama a tsakanin bangaren gwamnatin Yemen da ‘yan tawayen Houthis da suka dadde suna iko da garin na Mokha

Kakakin rundunar sojin kasar Mohammed Al Naqib ya ce sun yi nasarar fatatakar ‘yan tawayen da masu mara musu baya daga garin tare da karbe ikon babban tashar ruwan Mokha da ke da matukar mahinmanci ganin yana daya daga cikin tashoshin ruwan Yemen da ake anfani da shi wajen fitar da gahawar da ake nomawa a kasar.

An tabbatar da mutuwar ‘yan tawaye da masu mara musu baya ashirin da hudu da kuma soji 8.

Dubban farraren hula sun sami kansu cikin tsaka mai wuya a sanadiyar gumurzun.

Kafin kaddamar da farmakin kwato tashar ruwan ‘yan tawayen Houthis ne ke iko da kusan rabin gabar tekun Malia.

Al’ummar kasar Yemen fiye da miliyan goma sha bakwai ne ke fuskantar matsanancin yunwa baya ga miliyan kusan 7 da ke da bukatar agajin gaggawa sanadiyar yakin kasar na fiye da Shekaru biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.