Isa ga babban shafi
Myanmar

Fafaroma Francis ya nuna takaici kan halin da ake ciki a Myanmar

Shugaban darikar katolika fafaroma Francis ya bayyana takaici, kan halin kuncin da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya na Myanmar suke ciki, a yayin jawabinsa na mako mako.

Wasu masu gudun hijira`yan kabilar Ronhingya yayin wata zanga zangar adawa da shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi saboda kisan kare dangin da sojin kasar ke musu
Wasu masu gudun hijira`yan kabilar Ronhingya yayin wata zanga zangar adawa da shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi saboda kisan kare dangin da sojin kasar ke musu AFP
Talla

Fafaroma ya bayyana ‘yan kabilar Rohingya da mutanen kirki masu son zaman lafiya amman kuma ke fuskantar tsangwama daga gwamnatin kasarsu.

Bada daewa bane rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya zargi jami’an tsaron kasar ta Myanmar da laifin azabtarwa, kisa da kuma aikata fyade akan ‘yan kabilar Musulmin ta Rohingya, abin da Majalisar ta bayyana a matsayin aikata laifin kisan kare dangi.

A iyaka tsawon lokacin da aka shafe kawo yanzu rundunar soji da kuma gwamnatin Myanmar na cigaba da musanta zargin da ake na yiwa `yan kabilar kisan kare dangi, inda suka ce ana girmama al`amarin ne kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.