Isa ga babban shafi
Syria

An fara zirga-zirgar jiragen kasa a Aleppo

A Karon farko a cikin shekaru 4 mazauna birnin Aleppo da ke kasar Syria sun fara amfani da jirgin kasa wajen safara a birnin, sakamakon nasarar kakkabe mayakan ISIS da sojojin gwamnati suka yi.

Mutane sun fara dawowa Aleppo
Mutane sun fara dawowa Aleppo REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Rahotanni sun ce daruruwan mutane da suka hada da mata da maza da yara suka mamaye jirgin wanda ya ratsa ta Gabashin birnin mai dimbin tarihi.

Ministan sufurin Syria Ali Hamoud ya ce komawar aikin jirgin gagarumar nasara ce ga sojojin kasar wadanda suka sadaukar da rayukan su dan ceto birnin.

Tuni dai rayuwa ta fara dawowa daidai a gabashin Aleppo bayan sojojin gwamnati sun kwace ikon garin.

Rikicin Syria na tsawon shekaru 6 ya lakume rayukan mutane sama da dubu 300, tare da tursasawa miliyoya tserewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.