Isa ga babban shafi
Yemen

Saudiya ta kashe mutane dubu 10 a Yemen-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 10 Saudiya ta kashe a Yemen, tun lokacin da ta shiga yakin kasar don marawa Shugaba Abedrabbo Mansour baya don kakkabe ‘yan tawayen da ke kokarin tunbuke gwamantinsa.

MDD ta ce Saudiya ta kashe mutane dubu 10 a Yemen
MDD ta ce Saudiya ta kashe mutane dubu 10 a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Alkallumar na zuwa ne adai-dai lokacin da jakaden MDD a Yeman Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya gana a Aden da shugaba Abedrabbo Mansour Hadi kan dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta da lafar da kurar rikicin siyasar da ya taka rawa a yakin basasan kasar na shekaru biyu.

Saudiya ta shiga yakin Yemen ne a shekarar 2015 lokacin da shugaba hadi ya samu mafaka a kasarta.

Kakkakin MDD Farhan Haq ya ce yawan rayukan da suka salwata ya nuna bukatar gaggauta komawa teburin sulhu, yayin da fararren hula ke ci gaba da neman bukatar agaji.

Sai dai Shugaba Hadi ya yi watsi da daftarin da Ould Cheikh Ahmed jakaden MDD a Yeman ya gabatar na yiwuwar cim-ma zaman lafiya a kasar da ‘yan tawaye.

Daftarin ya bukaci samar da gwamantin hadin-kai da ficewar ‘yan tawaye daga birane kasar.

Shugaba Hadi na gani cewa amincewa da bukatar ta MDD a matsayin Sulhu zai disashe karfin mulkinsa da bai wa mataimakinsa Fifiko.

Yakin basasan Yemen ya kasance daya daga cikin mafi muni da ya tagayara al’umma a duniya a cewar MDD.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.