Isa ga babban shafi
Israel-Palestine

An tsayar da ranar taron sassanta rikicin Isra'ila da Falasdinu

Kasashen duniya akalla 70 ke shirin halartar wani taro da za a yi a birnin Paris na Faransa kan yadda za warware rikicin Isra’ila da Palasdinu, ta hanyar samar da kasashe biyu da za su rayuwa kafada-da-kafada.

Friministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas à  wata haduwa da suka yi a Jérusalem
Friministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas à wata haduwa da suka yi a Jérusalem AFP PHOTO/ALEX BRANDON-POOL
Talla

Taron wanda za a fara a ranar 15 ga watan gobe na Janairu, za a gudanar da shi ne ba tare da halartar wakilan Isra’ila ko kuma Falasdinu ba, to sai da Faransa wadda ke daukar nauyin taron ta ce tana da niyyar gayyatar Mahmoud Abbas da kuma Benyamin Netanyahu domin sanar da su abubuwan da aka tsayar a lokacin taron.

A wata sanarwa da ta fitar Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce kasar ta samu tabbaci daga kasashen fiye da 70 cewa za su halarci taron.

Yanzu haka dai ministan wajen kasar Jean-Marc Ayrault na gudanar da ziyara a birnin Beirut na Lebanon, kuma yana fatan samun goyon bayan kasashen yankin gabas ta tsakiya domin samun nasarar wannan taro na watan Janairu.

A can baya dai firaministan Isra’ila ya sa kafa ya yi fatali da wannan taro, yana cewa ba zai iya samar da mafita ga wannan rikici da ke tsakaninsu da Falasdinawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.