Isa ga babban shafi
Iran-Syria

Rouhani ya taya Assad Murna kan Aleppo

Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya taya shugaban kasar Syria Bashar al Assad murnar nasarar da ya samu wajen murkushe 'yan tawayen da suka mamaye birnin Aleppo.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Yayin tattaunawar da suka yi ta waya, shugaba Rouhani ya ce nasarar kama birnin Aleppo gagarumar nasarar ce ga mutanen Syria kan 'yan ta’adda da masu goya musu baya.

Shugaba Assad ya yaba da irin goyan bayan da Iran ke ci gaba da bai wa Syria wajen murkushe 'yan Ta’addan.

Rahotanni sun ce sojojin Iran da dama ne tare da sojojin sa kai daga kasar ke taimakawa gwamnatin Syria a Yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.