Isa ga babban shafi
Yemen

Kungiyar IS ta kashe sojoji 35 a Yemen

Akalla sojoji 35 ne suka rasa rayukansu yayin da kusan 50 suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake da kungiyar IS ta kaddamar a wani barikin soji da ke birnin Aden na kasar Yemen.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da harin wanda ya kashe sojoji 35 a birnin Aden na Yemen
Kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da harin wanda ya kashe sojoji 35 a birnin Aden na Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Dan kunar bakin waken ya kwance bama-baman da ya yi damara da su ne a dai dai lokacin da sojojin suka yi layi don karbar albashinsu na wata a barikin Al-Sawlaban

A ranar Litinin da ta gabata ne hukumomin Yemen suka kama mayakan IS guda takwas da ake zargi da kai wa jami’an tsaro hare-hare a cikin wannan shekarar.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne, dan kunar bakin waken IS ya kai hari da wata mota makare da bama-bamai, in da ya kashe mutane 71 a dai dai lokacin da sojoji ke atisayen daukar ma’aikata a birnin Aden.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.