Isa ga babban shafi
Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Suu Kyi ta ziyarci Rakhine

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ta ziyarci Jihar Rakhine, domin ganewa idonta yadda sojoji ke azabtar da kabilar Rohingya Musulmi, da basu da yawa a kasar.

'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar suna dakon samun izinin isa ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kuala Lumpur a Malaysia
'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar suna dakon samun izinin isa ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kuala Lumpur a Malaysia
Talla

Jakadan Majalisar na musamman Vijay Nambiar yace ganin yadda gwamnatin Myanmar ke ta kokarin kare kanta maimakon magance matsalar, na dada janyo mata suka daga sassan duniya.

Rahotanni sun ce sojojin sun kashe mutane da dama, hadi da yiwa mata fyade, sun kuma tilastawa akalla 20,000 tserewa zuwa kasar Bangladesh.

Sojin kasar dai sun ti rubdugu kan ‘yan kabilar ta Rohingya ne biyo bayan wasu hare hare da aka kai kan ofisoshin ‘yan sanda da ke kasar ta Myanmar a watan Oktoba.

Gwamnatin kasar Malaysia ta zargi gwamnatin Myanmar da aikata kisan kare dangi kan Musulmin ‘yan kabilar Rohingya, zargin da Myanmar ke cigaba da musawa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.