Isa ga babban shafi
Indonesia

Girgizar kasa ta kashe mutane 97 a Indonesia

Hukumomin Indonesia sun tabbatar da mutuwar mutane kusan 100 a girgizar kasa mai karfin maki 6.5 da ta auku a Lardin Aceh da ke kudancin kasar a yau Laraba.

Girgizar kasar Indonesia ta hallaka mutane kusan 100
Girgizar kasar Indonesia ta hallaka mutane kusan 100 Reuters/Aly Song
Talla

Shugaban rundunar sojin lardin, Tatang Sulaiman ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, kawo yanzu, mutane 97 ne suka rasa rayukansu kuma  adadin na ci gaba da karuwa.

Girgizar kasar ta faru ne a dai dai lokacin da musulmai ke shirin gudanar a sallar Asuba a tsibirin Sumatra, abin da ya jikkata jama’a da dama tare da ruguza daruruwan gidaje da masallatai.

Kazalika girgizar kasar ta shafi makarantun islamiyya da asibitoci da ke lardin, yayin da jama’a ke ci gaba da dari-darin faruwar ibtila’in Tsanami, lamarin da ya tilasta musu neman wuraren tsira tun da wuri.

A shekarar 2004 ne, ambaliyar ruwan Tsanami ta hallaka mutane dubu 170 a kasar Indonesia kawai, baya ga barnar da ta yi a wasu kasashe masu makwabtaka da tekun India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.