Isa ga babban shafi
Syria

Farraren hula na turmutsitsin ficewa daga Aleppo

Dakarun gwamnati sun kutsa kai a gabashin birnin Aleppo domin ci gaba da fatattakar ‘yan tawaye yayin da kasar Rasha ta bukaci kwashe fararen hula da ke fuskantar barazana sakamakon gumurzun da ake tafkawa a Syria.

Wasu da ke kokarin tserewa rikici a birnin Aleppo.
Wasu da ke kokarin tserewa rikici a birnin Aleppo. Reuters/路透社
Talla

Duk da sukar da kasashen duniya ke yi tare da gargadin Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a Aleppo, ana ci gaba da fuskantar barazanar mayar da birnin tamkar wata makekiyar makarbarta yayin da dakarun gwamnati ke ci gaba da dannawa da zummar karbe birnin baki daya daga hannun ‘yan tawaye.

Hare-heren birnin da suka hada da na makaman atilari, sun tirsasa wa dubban mutane kauracewa gidajensu musamman a yankin gabashi da ke karkashin kulawar ‘yan tawayen.

A halin yanzu dai dubban jama’ar da suka hada da maza da mata har ma da kananan yara na kwance akan tituna, in da akasarin su ke dauke da jakukkunansu na kayayyaki don tsere wa tashin hankalin.

Rahotanni sun ce, ana ci gaba da yi wa ‘yan tawayen lugudan wuta a dai dai lokacin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya kara ta’azzara gumurzun na yau.

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin kasar ta Syria ta ce, dakarun gwamnatin na rike da kashi 40 cikin 100 na yankin da ‘yan tawayen suka karbe a baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.