Isa ga babban shafi
China

Jam'iyyar Kwaminisanci na taro a China

Shugabannin jam’iyyar Kwaminisanci ta China da ta fi karfi a duniya na gudanar da taro a wannan Litinin a birnin Beijing da zimmar tattaunawa kan makomar jam’iyyar mai mambobi sama da miliyan 88.  

Jam'iyyar Kwaminisanci da ta fi karfi a duniya na gudanar da taro a birnin Beijing na China
Jam'iyyar Kwaminisanci da ta fi karfi a duniya na gudanar da taro a birnin Beijing na China
Talla

Kimaninin kusoshin jam’iyyar 400 ke tattauna a kasaitaccen Otel din Jinxing, in da za su shafe kwanaki hudu suna zantawa kan sauye-sauye a cikin jam’iyyrar da kuma yadda za a ci gaba da tafiyar da ita.

Kamfanin dillancin labaran China Xinhua ya ce, ganawar za ta mayar da hanakali kan batun bin doka da oda a jam’iyyar wadda ita ce mafi karfi a duniya.

To sai dai sanarwar da jam’iyyar ta fitar gabanin taron, ba ta bayyana irin zazzafar muhawar da za a iya tafka a taron ba, amma dai hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar gagarumin sauyi.

Tun lokacin da ya hau kan karagar mulkin kasar ta China, shugaba Xi Jinping wanda kuma sakatare janar ne na jam’iyyar, ke kokarin sauya tsarin jam’iyyar don cimma muradinsa.

Shugaba Jingping ya dauki jam’iyyar a matsayin makamin aiwatar da sauye-sauye don cimma muradinsa na sabonta China, abin da shugaban ke yawaita nanatawa.

Taron na yau dai, na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da jita-jitar cewa, da yiwuwar Jinping ya nemi tazarce bayan karewar wa’adinsa a shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.