Isa ga babban shafi
Syria

Kotun ICC zata binciki tauye hakki a birnin Aleppo

Shugaban sashin kula da kare hakkin dan’adam na Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad al Hussein, ya ce tilas a gabatarwa kotun hukunci kan manyan laifuka ta ICC halin da ake ciki a birinin Aleppo, domin fara gudanar da bincike.

Wani yanki a gabashin Aleppo da yaki ya rusa
Wani yanki a gabashin Aleppo da yaki ya rusa Mahmoud Hebbo/Reuters
Talla

Zeid Ra’ad al Hussein, ya sanar da hakan yayin wani taro na musamman na tattauna batun kare hakkin dan’adam, da Birtaniya ke jagoranta.

Makasudin taron dai shi ne kafa kwamiti na musamman da zai binciki tauye hakkin dan’adam da ya gudana a gabashin Aleppo.

Rahotanni sun ce, cikin wata guda bayan da sojin Syria hadi da goyon bayan Rasha suka kaddamar da sabon hari kan gabashin Aleppo, mutane 2000 ne suka samu munanan raunuka, yayinda sama da 700 suka rasa rayukansu.

Gwamnatin Syria ta dora alhakin samun yawan fararen hular da yakin ya ritsa da su kan ‘yan tawayen kasar.

Yanzu haka dai Majalisar Diinkin Duniya ta bayyana damuwa bisa yadda ta ce rashin tabbas na tsaron rayukan jami’an bada agaji, ya haifar da tsaiko ga kokarin da ake na kwashe fararen hula da ke gabshin Aleppo, bayan cimma tsagaita wutar awanni 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.