Isa ga babban shafi
Thailand

Sarkin Thailand mai dogon zamani ya rasu

Al’ummar Thailand na ci gaba da juyayin mutuwar Sarki Bhumibol Adulyadej da ya shafe tsawon shekaru 70 kan karagar mulki, Sarkin mai dogon zamani a duniya. A yau Alhamis ne Sarki Abdulyadej ya yi ban kwana da duniya yana mai shekaru 88 da haihuwa.

SarkinThailand Bhumibol Adulyadej
SarkinThailand Bhumibol Adulyadej REUTERS/Damir Sagolj/File Photo
Talla

Sarkin ya rasu ne a asibiti inda ya shafe shekaru biyu yana jinya.

Firaministan Prayut Chan-O-Chan ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi ga al’ummar Thailand. Kuma nan take ne ya nada dan shi Yarima Maha Vajiralongkorn a matsayi sabon Sarki

An haifi marigayi Sarki Adulyadej a ranar Litinin, 5 ga watan Disamban shekarar 1927 a asibiltin Mount Aurburn da ke Cambridge na Amurka, kuma shi ne dan auta ga iyayensa, yarima Mahidol Adulyadej da mahaifiyarsa mai suna Sangwan.

Bayan mahaifinsa a watan Satumban shekarar 1928, Adulyadej ya fara karatun Firamare a birnin Bangkok, sannan ya yi balaguro zuwa Switzerland don ci gaba da karatun sakandare, kafin daga bisani ya shiga jami’ar Lausanne, in da ya karanci ilimin kimiya.

Marigayin dai ya gaji sarauta ne yana da shekaru 18 bayan mutuwar yayansa mai suna Ananda Mahidol a shekarar 1946.

A shekara ta 1950 ne Adulyadej ya auri matarsa mai suna Rajawong Sirikit, wadda ta haifa masa yara hudu da suka hada da mata uku da namiji daya.

Gabanin mutuwarsa, marigayin shi ya fi ko wani sarki dadewa kan karagar mulki, in da ya shafe tsawon shekaru 70, yayin da Sarauniya Elizabeth ta Ingila da ta shafe shekaru 64 ke bi ma sa.

Ana dai kallon marigayin a matsayin ginshikin da ya rike Thailand musamman a lokacin rikice-rikicen siyasa, kuma tuni mahukuntan kasar suka ayyana zaman makoki na shekara guda don juyayin rasuwar Sarkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.