Isa ga babban shafi
Afghanistan

Hekmatyar na son zaman lafiya a Afghanistan

Tsohon shugaban 'yan tawayen Afghanistan Gulbuddin Hekmatyar ya bukaci samar da zaman lafiya a kasar bayan ya sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya da shugaba Ashraf Ghani.

Gulbuddin Hekmatyar, jagoran kungiyar  Hezb-e Islami ta Afghanistan
Gulbuddin Hekmatyar, jagoran kungiyar Hezb-e Islami ta Afghanistan DR
Talla

Hekmatyar da ke shugabancin kungiyar Hezb-i-Islam ya dade yana jagorantar yaki a kasar, abin da ya sa aka masa lakabi da ‘Butcher of Kabul'.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce, yanzu lokaci ya yi da kungiyar Taliban za ta yi nazari ko ta ci gaba da yakin ko kuma ta ajiye makamanta domin gina kasa.

Cikin wadanda suka halarci bikin sanya hannun a fadar shugaban kasar, sun hada da mataimakin shugaban kasa Abdallah Abdallah da tsohon shugaban kasa Hameed Karzai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.