Zafafa hari kan Aleppo ya raba mutane miliyan 2 da samun ruwa
Zafafa kai hari kan birnin Aleppo da sojojin Syria ke yi ya raba kimanin mutane miliyan biyu da samun ruwa.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabbin hare-haren da aka kaddamar ya lalata ilahirin tashar da ke tura ruwa zuwa abashin birnin na Aleppo da ke karkashin ikon ‘yan tawaye.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce domin kare tashar ruwan da ta yi saura daga lalacewa, dole aka rufe ta, kasancewar ita ke bawa sauran sassan birnin na Aleppo ruwa.
Wani mai magana da yawun sashin kula da yara na majalisar Dinkin Duniya Kieran Dwyer, ya ce rashin ruwan wata sabuwar barazana ce ga mazauna Aleppo, kasancewar shan ruwa marar tsafta zai haifar da barkewar cututtuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu