Isa ga babban shafi
Yemen

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 60

A safiyar yau litinin ce aka kai harin kunar bakin wake a sansanin horas da sojoji dake garin Aden, al’amarin ya yi sanadiyar mutuwar kuratan soji 60 tare da jikkata wasu 29.

Wani harin kunar bakin wake da kungiyar Al-qaeda ta kai a Yemen
Wani harin kunar bakin wake da kungiyar Al-qaeda ta kai a Yemen
Talla

Rahotanni na cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tuka wata karamar mota shake da ababen fashewa cikin sansanin Sojin a yayin da kuratan sojojin ke karbar horo.

Hukumomin kasar Yemen na cigaba da aikin horas da daruruwan sojoji da zummar kwato yankunan kasar daga hannun mayakan dake da’awar jihadi a kudancin kasar

Garin na Aden na fama da hare hare ta’addanci daga mayakan Al-Qeda da ISIL dake anfani da rudanin yaki a kasar wajen gudanar da ayyukansu.

Sai dai kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin na yau litinin.

Akalla mutane 6,600 ne suka mutu a tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu yawanci farraren hula ne, yayin da kasha 80 cikin 100 ke rayuwa cikin kunci sakamakon rikicin yakin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.