Turkiya ta kai hari kan mayakan Kurdawa
Rundunar mayakan Kurdawa da ‘yan tawayen Syria, ta ce jiragen yakin Turkiya sun yi luguden wuta kan muhimman wuraren da ke karkashinta dab da birnin Jarabulus da ta karbe daga mayakan IS.
Wallafawa ranar:
Mayakan sun kara da cewa harin jiragen Turkiyan ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama, lamarin da ta bayyana a matsayin tsokana.
Cikin satinnan ne dai rundunar sojin Turkiya da kaddamar da hare hare kan mayakan ISIL da na Kurdawa da ke cikin Syria.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ce kaddamar da hari kan 'yan ISIL da ke Syria ya zama dole don kare kasar daga hare-haren ta'addanci da ke karuwa a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu