Isa ga babban shafi
Syria

Mayakan 'yan tawaye da iyalansu sama da 300 sun fice daga Daraya

Kasashen Amurka da Russia sun sanar da samun cigaba a tattaunawa kan rikicin Syria. 

'Yan tawaye da fararen hula suna cigaba da ficewa daga Daraya
'Yan tawaye da fararen hula suna cigaba da ficewa daga Daraya SANA/Handout via REUTERS
Talla

Wakilan kasashen sun hadu ne a birni Geneva domin tattaunwa batun tsagaita wuta a kasar, kan rikicin da aka shafe shekaru Biyar ana yi tsakanin yan tawaye da dakarun Gwamnatin Shugaba Bashar Assad.

Ana gudanar da wannan zama tareda halartar mai shiga tsakani na musaman da Majalisar Dinkin Duniya ta nada Staffan De Mistura.

A gefe guda kuma yayin da ‘yan tawaye da fararen hula ke cigaba da ficewa daga birnin Daraya Jami’an sa ido a kasar Syria sun ce motocin biyar na farko dauke da mutanen sun isa birnin Idlib da ke hannun ‘yan tawayen kasar.

Kawo yanzu an samu nasarar kwashe mayakan ‘yan tawaye kimanin 300 tare da iyalansu daga Darayan, kuma ana sa ran kwashe karin 1000 daga birnin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.