Isa ga babban shafi
Philippines

An cinma tsagaita wuta tsakanin Gwamnati da 'Yan tawaye

Gwamnatin Philippines da 'yan tawayen Maoist da ke kasar, sun sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta yayin da suke cigaba da tattaunawar neman sulhu don kawo karshen daya daga cikin tada kayar baya mafi dadewa a nahiyar Asiya. 

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Talla

Sai dai mai bawa shugaban kasar Philippines shawara kan ayyukan samar da zaman lafiya Jesus Dureza ya ce akwai sauran aiki nan gaba kasancewar ba’a kammala tattaunawar ba.

Amincewar tsagaita wutar tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye ya shiga kundin tarihin kasar kasancewar ba’a taba cinma wannan nasara ba a baya.

Tun a ranar Litinin da ta gabata bangarorin biyu ke tattaunawa a birnin Oslo na kasar Norway kafin cinma wannan matsaya a ranar Juma’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.