Isa ga babban shafi
Turkiya

Shugaba Erdogan ya gargadi kasashen turai da Amruka kan katsalandan

A cikin wani jawabi da ya gabatar daga fadar shugaban kasar, Shugaba Erdogan ya ce wasu daga cikin kasashen Turai na bashi shawarwari kan cewa, sun damu amma shi abinda zai ce dasu shine su maida hankali akan abinda ya shafe su maimakon tsegumi da abinda ya shafi kasarsa. 

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan YASIN BULBUL / AFP
Talla

Shugaban kasar Turakiya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci kasashen Turai da Amruka da su kula da abinda ya shafesu mai makon katsalandan a cikin lamuran kasarsa,

Erdogan yace bisa dalilan jinkai ya watsar da daruruwan tuhume tuhumen da kotu ke yiwa wasu daga cikin wadanda aka zarga da hannu a shirya juyin mulkin.

Kawo yanzu dai Erdogan na tsare da mutane dubu 18 ne da suka hada da fararen hula da sojoji a karkashin yinkurin juyin mulkin da bai cimma nasara ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.