Isa ga babban shafi
Indonesia

Indonesia za ta harbe masu fataucin kwayoyi

Hukumomin Indonesia za su zartar da hukuncin kisa akan masu fataucin miyagun kwayoyi ta hanyar harbi, wannan kuma na zuwa ne bayan dakatar da zartar da hukuncin na wani lokaci.

Indonesia ta dawo da hukuncin harbe masu fataucin miyagun kwayoyi
Indonesia ta dawo da hukuncin harbe masu fataucin miyagun kwayoyi REUTERS/Beawiharta
Talla

Cikin wadanda za a zartar wa hukuncin akwai 'yan kasashen Najeriya da Pakistan da Zimbabwe, kuma nan da 'yan kwanaki ne za a harbe su a Indonesia bayan kama su da laifin fataucin maiyaghun kwayoyi.

Sai dai makhukuntan Indonesia sun ce babu wani dan nahiyar Turai da za a harbe, wanda shi ne karo na uku da ake harbe masu laifin a zamanin mulkin shugaba Joko Widodo.

Indonesia dai ta fuskanci matsin lamba daga kasahsen duniya bayan harbe wasu 'yan kasashen waje 7 ciki har da yan Asutralia biyu.

Amma shugaba Widodo ya jaddada cewa kasarsa na yaki ne da masu fataucin kwayu kuma ya zama wajibi su fuskanci hukunci mai tsauri.

Rahotanni sun ce, yanzu haka Indonesia ta fara shirin zartar da hukunci akan fursunonin, inda a jiya aka dauki dan Pakistan zuwa gidan yarin Java inda ake harbe mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.