Isa ga babban shafi
Syria

'Yan tawayen Syria sun harba roka a Damascus

'Yan tawayen Syria sun harba makamin roka tsakiyar birnin Damascus bayan wani kazamin harin da sojojin gwamnati suka kai asibitin garin Aleppo.

Mutane takwas sun mutu a harin Damascus na Syria
Mutane takwas sun mutu a harin Damascus na Syria Reuters/路透社
Talla

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria ta ce mutane 8 suka mutu a harin na Damascus yayin da wasu 20 suka samu raunuka.

Rahotanni sun ce an kai harin na Aleppo ne a asibtin Al Shaar inda aka kashe wani jariri mai kwanaki biyu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Syria a matsayin kasa mafi hadari ga jami’an kiwon lafiya, inda kididdiga ta nuna hare-hare 135 kan asibitoci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.