Adadin mamata ya karu a Afghanistan
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu a kasar Afghanistan a cikin watanni shida da suka gabata ya karu saboda yadda masu kai wa kasar hare-hare suka dada kaimi.
Wallafawa ranar:
Rahotan wanda ofishin majalisar da ke birnin Kabul ya fitar, ya nuna cewar tsakanin watan Janairu da Yuni na bana, an kashe fararen hula dubu 1 da 601 yayin da dubu 3 da 565 suka samu raunuka.
Wannan ya nuna cewar an samu karuwar kashi 4 cikin 100 na adadin mamatan da aka samu a shekarar 2015.
A jiya lahadi ne, al'ummar kasar suka yi zaman makoki don juyayin kazamin harin da kungiyar IS ta kaddamar kan masu zanga-zangar lumana a birnin Kabul, inda ta kashe mutane 84.
Shugaban kasar Asraf Ghani ya sha alwashin daukar fansa kan wadanda suka kitsa harin wanda aka bayyana a matsayin mafi muni da kasar ta Afghanistan ta gamu da shi a cikin shekaru 15.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu