Isa ga babban shafi
India

An yi wa masu fyade a India daurin rai da rai

Wata kotu da ke babban birnin Delhi na kasar India ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin daurin rai da rai bayan ta same su da laifin yi wa wata mata mai shekaru 52 fyade.

Masu zanga zangar adawa da fyade a India
Masu zanga zangar adawa da fyade a India REUTERS/Anindito Mukherjee
Talla

Matar dai ‘yar asalin kasar Denmark ce kuma ta ziyarci kasar ne domin yawon bude ido yayin da gungun kattin suka yi ma ta fashi tare da keta mutuncinta a watan Janairun shekara ta 2014.

A jumulce dai mutane tara aka kama hada da wasu yara masu kananan shekaru guda uku saboda zargin su da laifin, yayin da daya ga cikin su ya mutu gabanin kammala shari’ar amma har yanzu kananan yaran na ci gaba da fuskantar tuhuma a kotun hukunta laifukan yara.

Sai dai mutanen na da damar daukaka kara a babbar kotun kasar.

Hukumomin Delhi sun tsaurara sa ido kan masu fyde ne tun lokacin da wasu kattai suka yi wa wata daliba fyaden dangi a cikin motar fasinja a shekara ta 2012, abinda ya yi sanadin mutuwarta har lahira.

Fyaden 2012 ya haifar da zanga zanga tare da tilasta wa hukumomin kasar sauya dokar hukunta masu fyade a kasar.

Sai dai har yanzu, ana yawan samun rahotannin da ke nuna yadda ake ci gaba da yi wa ‘yan mata da kananan yara fyade a duk fadin kasar ta India.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.