Isa ga babban shafi
Amurka-Japan

Obama na ziyara a Hiroshima na Japan

A safiyar yau shugaban Amurka Barack ke ziyara a birnin Hiroshima na kasar Japan, wanda Amurka ta kai wa hari da makamin nukiliya a lokacin yakin duniya na biyu.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama da Friministan Japan Shinzo Abe
Shugaban kasar Amurka Barack Obama da Friministan Japan Shinzo Abe REUTERS/Toru Hanai
Talla

Hakan dai ya kasance na farko da wani shugaban na Amurka zai ziyarci wannan birnin bayan harin.

Obama wanda ke halartar taron kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a kasar ta Japan, zai ziyarci garin na Hiroshima tare da dora furanni a wani dandali domin tunawa da sama da mutane dubu 140, da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari da kasar ta kai a ranar 6 ga watan agustan shekara ta 1945.

Har ila yau an tsara shugaban na Amurka zai gabatar da wani kwarya-kwaryan jawabi dangane da wannan lamari, duk da cewa Obama ba zai nemi afuwar Japan a game da wannan hari ba.

Shugaba Obama dai na amfani da ‘yan watannin da suka rage masa a kan karagar mulki ne domin kai wannan ziyara a dai-dai lokacin da ake gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasar ta Amurka.

An jima ana tafka mahawara a game da harin na makamin nukiliya da Amurka ta kai a garin Hiroshima da kuma Nagasaki duk a kasar ta Japan, abin da wasu ke ganin cewa shi ne dalilin kawo karshen yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.