Isa ga babban shafi
Palisdinu

Falasinadawa sun yi watsi da bukatar Netanyahu kan zaman sulhu

Shugabannin Falasinadawa sun yi watsi da bukatar Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan shiga tattaunawar sulhu ta keke da keke a tsakaninsu ba tare da jagorancin Faransa ba.

Shugaban Palisdinawa Mahmud Abbas da Firaiyi Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Palisdinawa Mahmud Abbas da Firaiyi Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Mohamad Torokman/Sebastian Scheiner/Pool
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan Firaministan Faransa Manuel Valls ya gana da shugabannin bangarorin biyu da suka dadde suna fama da tashe tashen hankula a tsakaninsu.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na son a yi tattaunawar sulhu ce ta keke da keke tsakanin shi da shugaban Falisdinawa Mahmud Abbas maimakon zaman sulhun da Faransa ke shirin jagoranta a birnin Paris.

Amma Firaministan Falasdinawa Rami Hamdallah ya yi watsi da bukatar ta Netanyahu, yana mai cewa shugaban na Isra’ila na jan kafa ne ga yunkurin kasashen duniya na tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Hamdallah yace sun shafe shekaru sama da 20 suna tattaunawa amma babu wata nasara tsakaninsu da Isra’ila.

Wannan kuma na zuwa ne bayan Firaministan Faransa Manuel Vallas ya gana da shugabannin bangarorin biyu kan batun taron Paris.

A ranar 3 ga watan Yuni ne Faransa ta shirya jagorantar babban taro da zai kunshi ministocin harakokin wajen kasashen duniya da dama amma ba tare da wakilcin Isra’ila ba da Falasdinawa.

Sai daga baya taron zai gana da bangarorin biyu da nufin sasantawa wanda kuma ake ganin zai tabbatar da ‘yancin Falasdinawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.