Isa ga babban shafi
Faransa

An kama babban jami'in yansanda a Faransa

Wani shaida ya fallasa dabaru da hanyoyin da tsohon shugaban hukumar yaki da bazuwar miyagun kwayoyi ta kasar Faransa, Francois Thierry ke bi, wajen barin masu safarar miyagun kwayoyin shigowa da su a kasar

Hodar Iblis
Hodar Iblis
Talla

An gano hanyoyin da tsohon shugaban hukumar yaki da bazuwar miyagun kwayoyi Francois Thierry ke bi, wajen barin masu safarar miyagun kwayoyin shigowa da su a kasar.

Thierry na saukaka hanyoyin safarar ton ton na  hodar Iblis a Faransa tare da alaka da manyan masu safarar kwayoyi a nahiyar turai.

An fara bankado wannan bayanin ne a watan octobar bara, bayan da aka kama wata motar trela shakare da hodar iblis a tsakkiyar unguwar alfarma da’ira ta 16 dake birnin paris.

Kamun da jami’an tsaro suka yi, ya bada damar zakulo babban dilar mai suna Sofian H sananne ga hukumar ‘yan sandan, haka kuma daya daga cikin manyan masu safarar hodar iblis a nahiyar Turai, mutumin dake da alaka kai tsaye wajen samun bayanai da asirin daga shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyin François Thierry.

A tsawon shekaru 6 wannan mai samun bayanan asirin ‘yan sanda ya samu karfi da gindin zama ta yadda ako wane wata yake zazzage tan tan na  hodar iblis a birnin karkashin zura idon hukuma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.