Isa ga babban shafi
Syria

Ana ci gaba da luguden wuta a Aleppo

Har zuwa yau Litinin ana ci gana da ruwan wuta ta sama a yankin Aleppo na Syria, a yayin da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ke kokarin ganin an farfado da yarjejeniyar tsagaita wuta ta watanni biyu da aka amince a kasar a Geneva

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta ki yin tasiri a yankin Aleppo na Syria
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta ki yin tasiri a yankin Aleppo na Syria REUTERS/Abdalrhman Ismail
Talla

Tun a Lahadi ne John Kerry ya isa Geneva domin kokarin ganin an farfado da yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria.

Kuma bayan ya gana da jekadan Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura, da kuma ministan harakokin wajen Saudiya, John Kerry ya ce rikicin Syria al’amari ne da ya dami duniya wanda kuma har yanzu aka kasa shawo kansa.

Sai dai kuma Kerry ya ce da alamu akwai haske a tattaunawar farfado da yarjejeniyar tsagaita wutar da ake tattaunawa a Geneva. Kodayake rashin wakilcin Rasha a taron ya ragewa tattaunawar armashi ga bukatun da ake son cim ma.

Amurka dai ta bukaci Rasha ta tattauna da gwamnatin Assad kan tsagaita wuta.

Amurka da Rasha ne suka jagoranci yarjejeniyar da aka kulla a karshen Fabrairu. Amma daruruwan mutane ne aka kashe a luguden wutar da ake yi a Aleppo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.