Isa ga babban shafi
Iran

Masu sassauci ra’ayi sun yi nasara a zaben Iran

Bangaren Shugaba Hassan Rauhani masu sassaucin ra’ayi a Iran sun lashe zaben ‘Yan majalisu zagaye na biyu da aka gudanar a jiya Juma’a, kamar yadda aka sanar a hukumance a yau Assabar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Sakamakon zaben zagaye na biyu da ma’aikatar cikin gida ta sanar, ta ce Masu sassaucin ra’ayin sun samu kujeru 38 yayin da masu ra’ayin rikau suka samu kujeru 18

Wannan dai babbar nasara ce ga Shugaban Iran Hassan Rouhani da ke kokarin farfado da tattalin arzikin kasar bayan janye jerin takunkuman kasashen yammaci.

An dai je zagaye na biyu a zaben na ‘Yan majalisu a Iran saboda babu bangaren da ya samu kashi 25 na kuri’u a zagaye na farko da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.