Isa ga babban shafi
Syria

Jagoran 'yan adawar Syria zai shiga tattaunawar Geneva

Jagoran ‘yan adawar Syria kuma tsohon firaministan kasar, Riad Hijab zai halarci kasar Switzerland a yau laraba domin shiga tattaunawar zaman lafiya da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a birnin Geneva.

Shugaban 'yan adawar Syria  Riad Hijab
Shugaban 'yan adawar Syria Riad Hijab JACQUES DEMARTHON / AFP
Talla

An dai bayyana zuwansa a matsayin babbar nasarar diflomasiya da aka cimma da zai ga kawo karshen rikicin Syria da aka shafe shekaru biyar ana fama da shi .

A farko dai, wakilan gwamnatin Syria sun yi korafin cewa, rashin bayar da cikakken hadin kai daga shugabannin bangaren ‘yan adawa na daya daga cikin dalilan da suka hana ruwa gudu dangane da tattaunawar ta neman bakin zaren magance rikicin kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 250 tare da tilasta wa miliyoyin jama’a kaurace gidajensu inda suke naman mafaka a kasashen Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.