Isa ga babban shafi
Syria

ISIS ta hallaka fararen hula da sojoji a Syria

Wani hari da kungiyar ISIS mai da’awar jihadi ta kai a birnin Deir Ezzor da ke gabashin Syria ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 85 da kuma sojojin gwamnati 50 kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan hakkin adam a Syria ta sanar. 

Kungiyar ISIS na ci gaba da tayar da kayar baya a kasar Syria
Kungiyar ISIS na ci gaba da tayar da kayar baya a kasar Syria REUTERS/Murad Sezer
Talla

Shi kuwa kamfanin dillancin labaran Syria da ake kira SANA ya rawaito daga mazauna yankin cewa, kimamin fararan hula 300 ne suka rasu sakamakon farmakin na jiya Asabar.

Matukar dai aka tabbatar da haka, to lalllai zai kasance daya daga cikin manyan munanan hare haren da suka hallaka jama’a da dama a rana guda a cikin kusan shekaru biyar da aka kwashe ana fama da yaki a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.